Saturday, June 27, 2026
HomeIlimiGwamnatin Kano ta Kafa kwamitin mutum 9 domin tantance wadanda za'a tura...

Gwamnatin Kano ta Kafa kwamitin mutum 9 domin tantance wadanda za’a tura karatu waje

Date:

Gwamnatin Kano ta Kafa kwamitin mutum 9 domin tantance wadanda za’a tura karatu waje

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti mai mambobi tara domin tantance daliban dasuka aike da bukatarsu ta tafiya kasashen waje karo karatu cikin Shirin gwamnatin na daukar nauyin ‘yan asalin jihar domin karo karatu a jami’o’i daban daban na kasashen waje.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata shine yabayyana hakan yayin wani taron manema labarai daya gudana a ma’aikatar yada labarai ta Kano.

Dr Kofar Mata yace, izuwa yanzu sun karbi takardu fiyeda dubu daya da dari biyar (1,500) daga wadanda keda takardar digiri mai daraja ta daya, kuma tuni suka tantance mutum 800 daga cikin wancen adadi.

Dr Kofar Mata yacigaba da cewa, ” Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf ta kudiri aniyar tallafawa bangaren ilimi, shiyasa ake kokarin dorawa kan manufar tsohon Gwamnan kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na kai ‘yan asalin kano kasashen ketare domin yin digiri na biyu ko na uku”.

“Gwamnati a wannan lokaci zata dauki mutum dubu daya da daya (1,001), amatsayin matakin farko na shirin” Inji Dr Kofar Mata.

Kwamitin dai acewar kwamishinan, an bashi makwanni hudu ne yakammala aikin sa tareda mikawa gwamnati rahotonsa.

An tabayin makamancin wannan tsari dai a tsohuwar Gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories