Gwamnatin Kano ta Sallami kwamishinan Kasa da mashawarci akan matasa da wasanni
Gwamnatin Jihar Kano ta sallami kwamishinan Kasa da safiyo Alh Adamu Aliyu Kibiya daga kan mukaminsa bisa kalaman batanci ga alkalai da kuma mataimakin Shugaban kasa.
Awani taron Manema labarai da Gwamnatin ta kira, wanda kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye yajagoranta, Gwamnatin ta kuma Sallami Mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin matasa da Wasanni Amb Yusuf Imam ( OGAN BOYE).
Gwamnatin tace bada yawunta wadancen shugabanni sukayi abinda sukayi ba, inda ta nisanta kanta da kalaman da sukayi ga bangaran na shari’a da Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shattima.
Gwamnatin kanon ta kuma gargadi dukkanin Jami’anta dasu kiyayi furta kalamai wadanda basu shafi hukumomin da suke jagoranta ba.
An dai Jiyo tsohon Kwamishina Kibiya na wasu kalamai dake nuni ga alkalan dake jagorantar kotun sauraron korafin zaben Gwamna awani fefan bidiyo, yayinda agefe guda awani fefan bidiyon aka Jiyo Amb Yusuf Imam da akafi Sani da Ogan Boye na kalaman batanci ga Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shattima.