Thursday, April 30, 2026
HomeMuhalliGwamnatin Kano tace bazata lamunci zubar da shara akan tituna ba...Danzago

Gwamnatin Kano tace bazata lamunci zubar da shara akan tituna ba…Danzago

Date:

Gwamnatin jihar Kano tayi gargadi da kakausan harshe kan ma’aikatan duba gari wadanda suke umartar al’umma su fito da shara tare da jibge ta akan titunan birnin jihar nan.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago shine ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da ‘yan kasuwar kaji dake Kurna babban layi, a lokacin da ake kwashe musu sharar dake gab da kasuwar tasu.

Cikin Wani jawabi mai dauke dasa hannun Jami’in yada labaran hukumar Kamal Umar Kurna, Dan zago yace abin takaici ne yadda wadanda suke Kiran kansu da masu kula da kiwon lafiya Kuma a same su da umartar al’umma su zubar da shara akan tituna musamman wuraren da suke gudanar da rayuwar su ta yau da kullum.

Da suke bayyanawa shugaban hukumar kwashe sharar dalilinsu na zubar da shara a wajen tunda farko mazauna kasuwar sun ce ma’aikatan duba gari ne suka dinga zuwa kasuwar tare da umartarsu akan su fito da shara daga kwatoci da shagunansu tare da zubar da ita a gefen titin na babban layi, lamarin daya bawa al’ummar dake rayuwa a yankin damar mayar da wajen bola.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories