Gwamnatin jihar kano ta amince da fitar da kudin da yawansu ya zarce kimanin naira miliyan 39 domin biyan basussuakan da ma’aikatan wucin gadi na hukumar kwashe shara ta jihar nan suke bi na kimanin watanni 5.
Shugaban hukumar kwashe sharar ta jihar nan Ambasada Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai daya kira.
Dan zago yace biyo bayan tantancewa da kwamitin karta kwana da hukumar ta kafa ya gudanar, gwamnan kano Abba kabir yusif ya amince da biyan kudin domin inganta ayyukan tsaftar jihar kano ta hanyar biyan ma’aikatan hakkokinsu.
Dan zago yace kowane lokaci daga yanzu ma’aikatan wucin gadin zasu fara karbar kudinsu ta hanyar banki, tare da horansu dasu kasance masu kula da ayyuakansu a kowane lungu da sako na jihar nan da suka tsinci kansu domin gudanar da ayyukansu.