Har yanzu ba’a yanke hukunci akan sabbin masarautu ba….Abba Yusuf
Gwamnatin jihar Kano ta musanta labaran dake yawo a kafafen sadarwa na zamani akan yiwuwar rushe sabbin masarautu da gwamnatin baya ta kirkiro, inda tace har yanzu bata yanke hukunci akan matakin da zata dauka akansu ba.
Cikin wata sanarwa Jaridar DAILYFEEDSHAUSA ta samu mai dauke dasa hannun Sakataren yada labaran Gwamnan kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, gwamnatin tace mu’amalar aiki tsakanin bangaren zartaswa dana majalisa zata zama abude ne domin baiwa al’ummar Kano daman sanin meyake faruwa a gwamnatin da jami’iyyar NNPP kewa jagoranci.
Sanarwar ta Kara da cewa ” Maigirma Gwamna ya aikewa majalisar sunayen mashawarta na musamman guda 20 domin neman amincewarta, abinda majalisar ta amince dashi a zamanta na farko a yau.”
Ana saran mika sunayen kwamishinoni domin tantancewa a mako mai zuwa.
Jam’iyyar NNPP da Madugun kwankwasiyya sun sha sukar matakin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje kan kirkiro sabbin masarautu tareda tsige tsohon sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu.