Gamayyar kungiyoyin fararen hula karkashin inuwar KCSF tayi watsi da wasu rahotanni dake cewa an cire Ambasada Ibrahim A Waiya daga shugabancin gamayyar kungiyoyin.
Kungiyar, cikin wata takarda data fitar mai dauke dasa hannun Sakataren Kwamitin Amintattu na gamayyar kungiyoyin Alh Hamisu Isa Sharifai, ta bayyana matsayarta cewa babu wata kungiya ko wasu mutane da suka San da zamansu karkashin KCSF dake da iKon sakawa ko hanawa.
Sanarwar ta cigaba da cewa, “Dangane da batun zaben shugabanni, kwamitin amintattu ya kafa kwamiti makwanni uku da suka gabata domin shirya yadda zaben zai gudana nan bada jimawa ba.
A saboda haka, sanarwar ta Kara da cewa, daga nan har zuwa lokacin da za’a gudanar da zabe, Shugabannin Gamayyar kungiyoyin fararen hular karkashin jagorancin Ambasada Ibrahim Waiya sune halartattun shugabanni.
A karshe sanarwar tayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki musamman masu son cigaban gamayyar ta KCSF, dasu tashi tsaye tareda hade kawunansu domin samun nasarar zaben.