Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kano na binciken batan Naira Biliyan 100 a asusun kananan hukumomi
Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, yace hukumar na bin diddigi kan wasu kudade da hukumar ke zargin an karkatar dasu daga asusun kananan hukumomi cikin shekaru 6.
Muhyi Magaji ya bayyana hakan ne lokacin daya bayyana cikin Shirin “Akwana atashi a tashi” na gidan talabijin na Tambarin Hausa.
Yace,” wasu kudade ne na kananan hukumomin Kano 44 aka rika turawa ma’aji ma’aji na kananan hukumomin domin su Ciro tareda kaiwa wani mutum”.
“shi mutumin wanda keda injin kirga kudade a gidansa, ana kai masa kudaden ne tsabarsu inda daga nan shi kuma zai rabasu zuwa inda akeso araba” inji Barista Muhyi Rimin Gado.
Hukumar tace tuni bincikenta yayi nisa inda har ta gayyaci ma’aji ma’aji na kananan hukumomi domin amsa tambayoyi Wanda dazarar sun kammala bincike zasu gurfanar da wadanda abin ya yashafa gaban kotu.