Jam’iyyar APC a Kano ta gabatar da shaidu tara gaban kotun sauraran korafin zaben Gwamna
Kotun sauraron korafin zaben Gwamna a Kano dake zamanta a Miller Road, ta cigaba da sauraron shaidu da Jam’iyyar APC ke gabatarwa.
Ranar laraba a zaman kotun, Jam’iyyar APC ta gabatar da shaidu hudu, a talatar data gabata madai ta gabatarwa kotun shaidu hudu inda jumulla izuwa yanzu APCn ta gabatar da shaidu tara.
Dayake Karin bayani ga manema labarai Jim kadan bayan kammala zaman kotun na ranar laraba, lauyan dake kare Jam’iyyar ta APC Barista M A Lawan yace yanzu sun Kai ga gabatar da shaidu tara dag cikin fiyeda shaidu 300 da suke dasu “Kamar yadda kuka gani a yau mun gabatar da shaidu hudu kuma mun gamsu da irin tambayoyin da akai musu da irin amsoshin da suka bayar, yanzu muna da ragowar kwanaki tara daga cikin kwanaki 14 da kotu tabamu mu gabatar da shaidunmu” inji Barista M A Lawan lauyan APC.
Abangaren ta Jam’iyyar NNPP mai mulki tace ta gamsu da yadda shari’ar ke gudana, kuma basa shakka Jam’iyyar APC na bata lolacinta ne kawai.
Barita Bashir Yusuf Tudun Wuzirci gudane cikin lauyoyin dake kare NNPP da Gwamna Abba Kabir Yusuf, yace da sannu gaskiya zatayi halinta ” kamar yadda kuke gani sun gabatar da shaidu tara kuma daga yadda shaidun suke karyata sunayensu kunga ta tabbata basune wakilan da Jam’iyyar su ta tura gurin zaben ba” cewar Barita Bashir Tudun Wuzirci lauyan Jam’iyyar NNPP.
Jam’iyyar APC dai na kalubalantar NNPP da Gwamna Abba Kabir Yusuf kan nasarar daya samu a zaben da akayi awatan Maris din daya gabata.
Jam’iyyar APC a Kano, ta gabatar da shaidu tara gaban kotun sauraran korafin zaben Gwamna
Date: