Gwamnatin jihar Kano tace shirye shirye sunyi nisa wajen inganta harkokin sufuri da zirga zirga a fadin jihar.
Mataimakin Gwamna Comrade Aminu Abdulsalam shine yabayyana hakan lokacin kaddamar da Sabon kamfanin hada hadar sufuri na Sweetride daya gudana a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari.
Mataimakin Gwamnan wanda yasamu wakilcin babbar sakatariya a Ma’aikatar sufuri Hajiya Amina Muhammad Usman, tace sunyi zama na musamman da Kamfanin akan inganta tsarin na sufuri tareda samar da tsaron lafiya fasinjoji da matuka ababen hawa.
Anasa bangaren shugaban Kamfanin na Sweetride Alh Ibrahim Yusuf Gobir, yace, kamfanin zaiyi mu’amala ne da masu babura masu kafa uku da motoci wadanda sukayi rajista da Kamfanin ta yadda fasinja zai iya kiran abin hawa daga gida ta hanyar amfani da MANHAJAR da suka samar.
Bayaga haka acewar Yusuf Gobir, akwai tsarin samar da tsaro ga matuka ababen hawan aduk lokacin da suka fuskanci wata barazana daga bata gari.
Kamfanin dai yaraba wayoyin hannu akalla dubu biyar ga masu ababen hawan na mota da baburan adaidaita sahu domin gudanar da ayyukansu cikin sauki.