Tsohon Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace kofarsa abude take domin yin sulhu da abokin hamayyarsa na siyasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Dr Ganduje ya bayyana hakan lokacin dayake ganawa da manema labarai ciki harda Wakilin DAILYFEEDSHAUSA.
Ganduje wanda shine sabon shugaban Jam’iyyar APC na kasa, yace baya gaba da Kwankwaso hasalima akwai zumunci mai karfi da soyayya tsakaninsa da mahaifin Kwankwaso marigayi Makaman Karaye, inda yace ko bayan rasuwarsa shine yatsaya tsayin daka aka bar sarautar a gidansu.
“Mutane da yawa sunso adauke sarautar daga gidan, to amma naki amincewa inda nasa aka baiwa kaninsa wanda a lokacin dagaci ne”, cewar Dr Abdullahi Ganduje.
Ganduje yakara da cewa, akwai lokacin da yana Gwamnan kano yakan Kai ziyara domin duba dan Kwankwaso dayake zaune a hadaddiyar daular larabawa (Dubai) domin karfafa zumunci.
Alaka dai tayi tsami tsakanin tsoffin gwamnonin biyu duk kuwa da dadewa da sukayi tare amatsayina abokan siyasa, inda har Ganduje yayiwa Kwankwaso mataimaki har sau biyu.