Thursday, April 30, 2026
HomeNomaKungiyar KEBBI DALA FARMERS ta tallafawa Manoma da wayoyin hannu

Kungiyar KEBBI DALA FARMERS ta tallafawa Manoma da wayoyin hannu

Date:

Kungiyar KEBBI DALA FARMERS ta tallafawa manoma

Kungiyar “Kebbi Dala Farmers”, ta tallafawa manoma da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya da kayan noma da wayoyin hannu da zasuyi amfani dasu domin kara samun ilimi abangaren na noma.

Kungiyar ta ” Kebbi Dala Farmers” dake da rassa a jihohi 17 na Arewacin Najeriya, nada manufar ingantawa da saukakawa manoma samun kayan aikin gona kamar iri da takin zamani acikin farashi mai sauki.

Acewar shugaban kungiyar Comrade Habib S Umar, an samar da kungiyar ne domin saukakawa manoma,” an samar da wannan kungiya domin baiwa manoma horo da kuma samar musu da kayan noma cikin farashi mai sauki” inji Comrade Habib.

Comrade Habib yacigaba da cewa” Muna basu damar ajiye kayan amfanin gonarsu har lokacin da kayan noman zasuyi darajar da zasu maida abinda suka kashe”.

“Kuma idan mun basu bashi suna biyanmu ne da kayan noma, ragowar kuma sunada damar siyar mana ko su saidawa wasu, ko kuma mu ajiye musu” Comrade Habib S Umar.

Kungiyar dai tayi hadin gwiwa ne da Kamfanin “Tingo Mobile” domin baiwa manoman bashin wayar hannu cikin farashi mai sauki, da kuma tsarin biya cikin shekara biyu.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories