Kungiyar Kwallon kafa ta CMC ta lashe gasar da kamfanin Century Mining yasaka
Gasar da kamfanin Century Mining Company yashirya ga kungiyoyin kwallon kafa na karamar hukumar Doguwa tazo karshe, inda aka buga wasan karshe a ranar lahadi.
An dai fafata ne a wasan karshe tsakanin kungiyar kwallon kafa ta CMC da Young Stars FC inda aka tashi canjaras sai dai CMC ta lashe wasan a bugun daga Kai sai mai tsaron raga.
Tunda fari a ranar asabar an buga wasan neman na uku tsakanin Shooting Stars FC da Kungiyar Mai Saje FC wanda akarshe kungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars ta samu nasarar zama na uku.
A dai fara gasar ne tun awatan Nuwamban daya gabata karkashin kulawar kamfanin Century Mining da nufin zaburar da matasa a mataki na kasa.