Tuesday, August 25, 2026
HomeLabaraiKungiyar mamallaka kafafen yada labarai ta NBMOA ta nada Abbas Dalhatu Shugaban...

Kungiyar mamallaka kafafen yada labarai ta NBMOA ta nada Abbas Dalhatu Shugaban riko

Date:

Ƙungiyar mamallaka kafafen yaɗa labarai ta Arewacin ƙasar nan NBMOA ta ƙaddamar da kwamitin riƙon da zai jagoranci babban taronta na shekara-shekara tare da zaɓar sabbin shugabanni.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar aka rabawa kafafen yada labarai ciki harda DAILYFEEDSHAUSA, Ƙungiyar ta naɗa Alhaji Abbas Ɗalhatu, Shugaban rukunin tashoshin Freedom Radio da Dala FM a matsayin shugaban Kwamitin riƙon.

Sai Hajiya Maimuna Yahaya shugabar gidan rediyon WE FM a matsayin Sakatariyar kwamitin.

A Jumu’ar da ta gabata ne shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar Dakta Ahmed Tijjani Ramalan ya ƙaddamar da Kwamitin riƙon a birnin tarayya Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin tsoffin shugabannin ƙungiyar wanda Shugaban tashoshin Unity Radio da Talabijin Alhaji Salihu Dasuƙi Nakande ya jagoranta.

Ana sa ran Kwamitin riƙon zai tsara yadda za a iya gabatar da babban taron ƙungiyar na shekara-shekara da yin zaɓe ido da ido ko kuma ta hanyar fasahar zamani.

Kazalika, Kwamitin riƙon zai samar da shawarwarin da za a yi gyare-gyare a Kundin tsarin mulkin ƙungiyar.

An dai samar da kungiyar ne da nufin samar da wani dandali da mamallaka kafafen yada labarai a arewacin Najeriya zasu rika haduwa domin tattauna kalubalen da suke fuskanta tareda samar da mafita.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories