Friday, June 26, 2026
HomeShari'aKwamishinan 'yansandan Kano yakai ziyara ga babbar jojin Kano

Kwamishinan ‘yansandan Kano yakai ziyara ga babbar jojin Kano

Date:

Kwamishinan ‘yansandan Kano yakai ziyara ga babbar jojin Kano

Babbar Jojin Kano Hon Justice Dije Aboki ta karbi bakuncin Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano CP Muhd Usaini Gumel da ‘yan tawagarsa.

Kwamishinan ‘yansandan ya bayyana ziyarar amatsayin ta sada zumunci da taya murna ga Justice Dije Aboki bisa zamowarta babbar jojin Kano ta rikon kwarya, inda yace an saka kwarya a gurbinta.

CP Gumel yayi da samun Karin fahimtar juna tsakanin Jami’an ‘yansanda da bangaren shari’a domin cigaba da kare jihar kano tareda kawo karshen fashin waya, yana mai cewa tuni suka kama tareda gurfanar da fiyeda ‘yan fashin waya 400.

Cikin wani jawabi da aka rabawa manema labarai ciki harda DAILYFEEDS mai dauke dasa hannun kakakin babbar kotun Kano Baba Jibo Ibrahim, yace datake maida jawabi, babbar jojin Kano Justice Dije Aboki ta bayyana farin cikinta da ziyarar da kwamishinan ‘yansandan yakawo mata tareda yaba masa bisa kokarin dayake wajen kawo karshen fashin waya da sauran miyagun laifuka da ake aiwatarwa

Babbar Jojin ta Kuma yi kira ga ‘yansanda dasu daina dogaro da shaidar amsa laifi daga bakin masu aikata laifin kadai, inda ta shawarcesu dasu rika Kai ziyara inda aka aikata laifin, tare kuma da karbar shaidar wanda ake zargi da yarensa kafin akaiga fassarawa.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories