Friday, June 26, 2026
HomeLabaraiKwankwaso Ba Shi da Hurumin Ba da Shawarar Janye Tsaron Sarkin Kano...

Kwankwaso Ba Shi da Hurumin Ba da Shawarar Janye Tsaron Sarkin Kano –  Babba Dan Agundi

Date:

Kwankwaso Ba Shi da Hurumin Ba da Shawarar Janye Tsaron Sarkin Kano –  Babba Dan Agundi

Sarkin Dawaki Babba Alh Aminu Babba Dan Agundi , ya yi kakkausar suka ga kalaman da tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi dangane da batun janye jami’an tsaron da ke kula da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Dan Agundi ya bayyana cewa Kwankwaso ba shi da wani hurumi ko ikon yin magana ko ba da shawara a kan tsaron Sarkin Kano, yana mai jaddada cewa wannan batu yana gaban kotu.

A cewarsa, duk wata magana da ake yi a kai a halin yanzu ba ta da tushe, domin al’amari ne da ke jiran hukuncin shari’a.

Ya kara da cewa ba Kwankwaso kadai ba, hatta Gwamnan Jihar Kano ma ba shi da hurumin janye jami’an tsaron na Alh Aminu Ado Bayero.

Sarkin Dawaki Babba ya bayyana cewa kotu ce ta bayar da umarnin samar da tsaro ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ba gwamnati ba.

Dan Agundi ya bayyana kalaman da Kwankwaso ya yi a matsayin marasa muhimmanci, yana kwatanta su da “zancen teburin mai shayi,” wato magana da ba ta da tasiri ko daraja a tsarin doka.

A karshe, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya bukaci a mutunta doka da kotu, tare da kaucewa furucin da ka iya tayar da hankali ko rikita al’umma.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories