Thursday, April 30, 2026
HomeLabaraiMaimartaba Sarkin Kano ya amince da nadin Sabon Sarkin Hatsin Kano

Maimartaba Sarkin Kano ya amince da nadin Sabon Sarkin Hatsin Kano

Date:

Mai martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero, ya amince da nadin Galadiman Sarkin Dogaran Kano, da kuma Sarkin Hatsin Kano.

An nada Sabon Sarkin Hatsin na Kano ne da Galadiman Sarkin Dogaran bisa amincewa da Umarnin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR.

An dai gudanar da nadin Sarautar ne a karkashin jagoranci Shamakin Kano Alhaji Wada Najalo, wanda aka nada Sarkin Hatsin Kano Alhaji Bello Sani Abubakar, a Soron Sarkin Hatsi.

Shi kuwa Sabon Galadiman Dogaran Kano Alhaji Ibrahim Mahmud Dogarai, anyi nadinsa ne a gidan Sarkin Dogaran Kano.

Cikin wani jawabi mai dauke dasa hannun Sakataren yada labaran Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’Isa, ya rawaito Shamakin Kano Alhaji Wada Najalo, najan hankalin wadanda aka nada da cewa su rubanya ayyukansu ta hanyar cigaba da yin biyayya da bin umarnin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Yace an nada su wadannan sarautu ne biyo bayan rasuwar da wadanda suke da mukaman sukayi, wanda aka maye gurabansu dasu.

Yace Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya su murna tareda fatan alheri da cigaba da rike Martabar Masarautar Kano mai cike da tarihin da take dashi.

Kafin wannan nadin dai Alhaji Bello Sani Abubakar shine ciroman Sarkin Hatsi inda yanzu ya zama Sarkin Hatsin Kano, yayin da Alhaji Ibrahim Mahmud yake a Matsayin Ciroman Sarkin Dogarai, yanzu kuma ya zama Galadiman Dogaran Kano.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories