Wednesday, August 26, 2026
HomeDa Ɗumi-ƊumiMajalisar Dinkin duniya ta gayyaci tsohon Gwamnan kano Shekarau

Majalisar Dinkin duniya ta gayyaci tsohon Gwamnan kano Shekarau

Date:

Majalisar Dinkin duniya ta gayyaci tsohon Gwamnan kano Shekarau

Rahoto dake yawo a kafafen sadarwa na zamani dake cewa Majalisar dinkin duniya ta baiwa tsohon Gwamnan kano Sanata Ibrahim Shekarau mukami na cigaba da bazuwa.

Wannan tasanya Jaridar DAILYFEEDSHAUSA tayi kokarin Jin tabakin tsohon Gwamnan inda ya aiko da sakon karta kwana ta hannun mai taimaka masa Jibril Muhd Natara dake tabbatar da cewa Majalisar dinkin duniya ta aiko masa da gayyata.

Sakon na cewa “tabbas na samu gayyata daga Sakatare janar na majalisar dinkin duniya wani lokaci cikin watannan inda yabukaci naje birnin New York domin wata ganawa, amma dai bani da cikakken bayani akan abinda zai faru sai dai cikin mako mai zuwa zan amsa gayyatar zuwa Amurka.”

Sanata Shekarau dai yayi gwamnan jihar Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya sau biyu, yayi Ministan Ilimin kasar lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kafin yazama Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a shekarar 2019 na wa’adi guda daya kammala makon daya gabata.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories