Thursday, April 30, 2026
HomeMuhalliMajalisar dokokin Kano ta nuna gamsuwarta da ayyukan REMASAB

Majalisar dokokin Kano ta nuna gamsuwarta da ayyukan REMASAB

Date:

Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana gamsuwar ta bisa yadda aikin kwashe shara yake gudana a fadin jihar.

Shugaban Majalisar Rt Hon, Isma’il Jibril Falgore ne ya bayyana hakan lokacin da tawagarsa ta gamu da ma’aikatan hukumar kwashe sharar jihar bisa jagorancin shugaban hukumar Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago a unguwar ja’in.

Hon, Jibrin yace duba da yadda Dan zago yake gudanar da aikinsa tun bayan daya karbi hukumar wajen tsaftace birnin Kano da kewayen sa, ya zama wajibi a Yaba masa domin Kara masa kaimi wajen tafiyar da hukumar.

Da yake nasa jawabin tun da farko shugaban hukumar kwashe sharar ta jihar kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago, yace aikin da hukumar sa take gabatarwa abu ne daya zama wajibi matukar anasan cigaban Kano tare da bukatar ‘yan majalisaun jihar nan dasu bayyanawa hukumarsa duk Wani abu Wanda suke ganin hukumar tasa ta kaucewa ka’ida domin gyarawa.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories