Man United ta lashe wasanta na farko a gasar premier ta Ingila
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta lashe wasanta na farko a gasar premier.
Kungiyar ta samu nasarane ta hannun dan wasanta na baya Rafael Varane wanda ya zura kwallo a mintuna na 76 bayan da yasamu taimako daga dan wasan baya Wan Bissaka.
Ta dai samu nasarane akan kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton Wonderers a wasan karshe na wasannin makon farko na gasar ta premier ta shekarar 2023/2024.
A mintuna na 95 mai tsaron ragar Manchester Onana ya bige dan wasan Wolves a cikin yadi na 18, to sai dai alkalin wasa Simon Hooper yace Babu abinda yafaru, abinda yajanyo Cece kuce daya hasala mai horar da ‘yan wasan Wolves Gary O’Neal wanda takaiga alkalin wasa Hooper ya bashi Katin gargadi.
Masu sharhi dai na ganin cewa har yanzu Manchester United nada aiki ja agabanta duk da sabbin ‘yan wasa data cefano irinsu Mason Mount da Onana, idan akayi la’akari da abokinyar hammayarta Manchester City.