Babban mai taimakawa gwamanan jihar Kano kan ababan hawa na Jihar kano, Alhaji Musa Isah (Peugeot) ya mika godiyarsa ga mai girma gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa zaben sa da yayi a matsayin babban mataimaki na musamman wajen farfado da sha’anin ababen hawa a Jihar Kano.
Musa Peugeot ya ce wannan matsayi da Allah Ya bashi, zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya inganta harkokin sufuri domin kawo cigaban Jihar Kano, kasancewar ta cibiyar kasuwanci a fadin Najeriya.
Alhaji Musa Isah, ya ce zai yi aiki da dukkannin shugabanin kungiyoyi da kamfanoni da masana’antu musamman wadanda suke kera ababen hawa – domin kawo sauyi ta hanyar zamani a sha’anin sufuri da nufin inganta kasuwanci a Jihar Kano.
Peugeot yace wannan matsayi da Allah Ya ba shi zai yi amfani da shi domin ganin ya shigo da matasa cikin sha’anin harkokin sufuri don su dogara da kansu ta hanyar samar musu da kyakkyawar rayuwa.
Ya kara da cewa harkar sufuri na daya daga cikin hanyoyin dake Bunkasa tattalin arziki akasashen duniya.
Ya kuma bukaci daukacin yan kasuwa da masu masana’antu da su hada kai da kamfanoni manya da kanana domin bai wa gwamnati hadin kai a lokacin da offishinsa zai fara gudanar da aiki wanda hakan zai taimaka sosai ta fannin kawo gyara a sha’anin Bunkasa sufuri da kasuwanci a jihar kano.
Musa Peugeot ya kuma yi fatan alkhairi da fatan samun nasarar gwamnatin Alh. Abba Kabir Yusuf da addu’ar Zaman a Jihar Kano.
Akarshe yataya Al’ummar Nigeria murnar cika shekara (63) da samun yancin kai tare da meman addu’ar Zaman lafiya DA karuwar arziki a jihar Kano Dama kasa baki daya.
Mataimakin Gwamna Abba Kabir Akan Harkokin Ababen Hawa Yayi Alwashin Inganta Harkokin Sufuri A Kano
Date: