…sai nan gaba mutanen Kano za su fahimci cewa Gwamna Abba Kabir don cigaban al’uma yake daukar wadannan matakan
…wajibi Gwamnatin Kano ta tsawatarwa da ma su sukar ta da kalaman batanci da labaran karya
Biyo bayan korafe-karafen da wadansu daga cikin al’umar Kano suke yi dangane da matakin da Gwamnan Kano, Engr Abba Kabir Yusuf, yake dauka na rushe gine-ginen da tsohuwar Gwamnatin Ganduje ta baiwa makusantan ta ba bisa ka’ida ba, wani makusancin gwamnan, Alhaji Bashir kuma Shugaban Kungiyar AKY Brotherhood Campaign 2023, ya mayar masu da martani – inda yace “da yawan ma su sukar matakin gwamnan, ba masoya cigaban jihar Kano bane.”
Alhaji Bashir, wanda ya zanta da Jaridar Daily Feeds Hausa a ranar Asabar 10 ga watan 6 na shekarar 2023, ya zargi ma su ganin baiken sabon gwamnan da nuna alamun kin gaskiya, da goyon bayan ma su yunkurin lalata tarihi da martabar jihar Kano.
Ya koka cewar da yawa mutanen da suke yin fito-na-fito da rushe haramtattun gine-ginen da Gwamna Abba yake yi, sune a baya suka yiwa Gwamnatin Ganduje tofin Allah Ya tsine, inda yace sauya ra’ayin da suka yi, tare da rungumar rashin gaskiya, abin takaici ne.
Ya tuna cewa Gwamnatin Ganduje, tunda da farko, itace ta dauki gabarar cefanar da filayen jihar Kano – wadanda a ka’ida an samar da su ne domin amfanuwar jama’ar jihar Kano “ba wai gine-gine, ko filaye ne da aka ajiya a matsayin kadara – wacce wani shugaba zai wayi gari; ya mallakawa kansa, da iyalansa da kuma makusantansa ba.”
“Kano a halin yanzu, jajirtaccen shugaba take so – wanda ba bu niyya, ko tunanin sayar da ‘yancin al’uma a ransa, ko kuma aikata laifukan da mutuncinsu zai zube a idanun Duniya. Daga cikin abubuwan takaicin da tsohon gwamna, Ganduje, yayi cikin shekaru takwas har da sarayar da mutuncin mutanen Kano, sakamakon bata sunan jihar da yayi akan sha’anin Dalar Amurka – mutanen jihohin kasar nan (musamman na Kudanci) suka yi mana kudin-goro.”
A baya-bayan nan ne dai aka ji tsohon gwamnan yana kare kansa cewa “ai ko Masallacin Harami na Makkah, a zagaye yake da shaguna sabida haka, ba wani laifi don an zagaye Masallacin Idi da shaguna…” sai dai Makusancin Gwamnan, Alhaji Bashir, ya kalubalanci Ganduje cewar kuskure babba, a rika jin mutumin da yake da ilimi, yana fadar wannan maganar – la;akari da cewar akwai bambanci tsakanin Masallacin Harami da zagaye shi da akayi da shaguna; da kuma abinda Ganduje ya yiwa Babban Masallain Idin Kano.
“Babban misalign da yake bambanta abinda Ganduje yayi, da wanda mahukunta a Kasar Saudiyya suka yi shine, shagunan jikin Masallacin Harami ba wani ne a cikin Sarakunan Saudiyya ya sayarwa ‘yan korensa, ko matansa da ‘ya’yansa ba – suka gina domin karbar kudin haya; ko kuma sayarwa da wadansu ba. Shaguna ne mallakin Masallaci, wadanda ake yin amfani da kudin da ake sa mu ta hanyoyin su, domin kula da sha’anin Masallaci. Kuma ba haka Ganduje yayi ba.”
“A iya ka abinda al’uma suka fahimta a jihar Kano shine, duk kudaden da aka sayar da filayen nan, musamman na Babban Masallacin Idi, ba bu inda akayi amfani da su wajen sake gyara shi, ko kuma a yiwa al’uma wani aikin da shi. Kudi ne kawai da yake shigewa cikin aljihun gwamna da iyalansa, da kuma ‘yan-korensa. Sa’annan ba bu maganar lissafin nan gaba al’umar jihar Kano karuwa suke yi, sabida haka wannan fili girma ya fi dacewa ma a kara masa – a’a su abinda suke hange kawai shine ina wani fili yake a cikin gari su sayar da shi; su jefa kudin cikin aljihunsu – idan yaso kowa ma ya mutu.”
Alhaji Bashir, wanda ya yabawa Gwamna Abba Kabir din bisa cikawa al’umar jihar Kano da yake yi na kwato masu hakkokinsu – wadanda tsohon gwamna ya kwace; ya kumaa godewa Sanata Rabi;u Musa Kwankwaso bisa bayanan da yayi akan matakin gwamnatin Kano na rushe gine-ginen da Abba yake yi.
“Sabida haka a shawarce, mutanen jihar Kano murna ya kamata su rika yi a halin yanzu, tare da yiwa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara – domin rashin yin hakan alamu ne dake nuna cewa ba mu shirya samun cigaba a jihar mu ba.”
Da yake jaddada goyon bayan sa akan matakin da sabon gwamnan yake dauka, wanda a cewar sa, sai nan gaba al’umar jihar Kano za su fahimci alherin daAbba Gida-Gida yake nufin su da shi, ya rokin Gwamnatin Kano da dauki matakin ladabtarwa ga Dan-Bilki Kwamanda akan sakin bakin da yake yiwa Gwamnatin Abba a Kano, inda har ya kara da cewa barin mutane suna furta kalaman rashin ladabi ga shugabanni, abu ne da zai lalata tarbiyar matasan, da rashin ganin girman shugabanni.
Ya kuma shawarci al’umar Kano da suyi watsi da rade-radin da akayi ta yayatawa cewar Fadar Shugaban Kasa ta dakatar da rushe haramtattun gine-gine a Kano.