Thursday, April 30, 2026
HomeBikin SallahSadiq Wali ya taya al'ummar Kano murnar barka da Sallah Babba

Sadiq Wali ya taya al’ummar Kano murnar barka da Sallah Babba

Date:

Sadiq Wali ya taya al’ummar Kano murnar barka da Sallah Babba

Dantakarar Gwamnan Kano na Jam’iyyar PDP a zabe daya gabata Hon Sadiq Aminu Wali, ya aike da sakon taya murna da barka da Sallah ga al’ummar jihar Kano.

Cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun sa, Hon Wali yayi nuni da cewa, Idin Babbar Sallah ko kuma Sallar layya lokaci ne na tunawa da sadaukarwa da imani da Annabi Ibrahim A S ya nuna.

Yakara da cewa, lokaci ne da iyalai da abokai d sauran jama’a zasu hadu domin samar da hadin kai tareda taimakon juna da jinkai.

Dayake magana kan zaben daya gabata, Sadiq Wali yace” Duk dayake zaben Gwamna na shekarar 2023 baizo yadda akai tsammaninsa ba ga Jam’iyyar PDP, to amma ya zama wajibi na nuna godiyata ga goyon baya da amincewa da al’ummar Kano suka nuna min.”

Yace,” Amincewarku da manufofinmu na samar da rayuwar gaba mai kyau, abun ayaba ne, a saboda haka zan cigaba da aiki tukuru tareda sadaukar dakai wajen inganta rayuwar al’ummar mu ta Kano”.

Sadiq Wali wanda yataba rike mukamin Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, ya tabbatarwa da mutanen Kano cewa duk da yadda sakamakon zabe ya kasance, bazai gajiya ba wajen ya faranta al’ummar ta Kano.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories