Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaSanata Godswill Akfabio ya zama shugaban majalisar Dattawa ta goma.

Sanata Godswill Akfabio ya zama shugaban majalisar Dattawa ta goma.

Date:

Sanata Godswill Akfabio ya zama shugaban majalisar Dattawa ta goma.

‘yan majalisar Dattawa sun zabi Sanata Godswill Akfabio daga jihar Akwa Ibom amatsayin sabon shugaban majalisar.

Sanata Akfabio ya fafata da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’Aziz Yari, inda Akfabio yasamu kuri’u 63 yayinda Yari yasamu kuri’u 46.

Wannan dai kusan itace fafatawa mafi karfi da akayi abaya bayannan wajen neman shugabancin majalisar ta dattawa, a inda Sanata Abdul’Aziz Yari yaki amincewa da janyewa Sanata Akfabio akokarin sulhuntawa da samar da daidaito da Jam’iyyar APC tayi kokarin yi.

Sanata Akfabio dai ya Mulki jihar Akwa Ibom har na wa’adi biyu kafin zabar sa zuwa babbar majalisar ta Dattawa.

Awani cigaban kuma, an zabi Sanata Barau I Jibrin daga Jihar Kano amatsayin mataimakin shugaban majalisar ta Dattawa.

Sanata Barau tunda fari ya nemi kujerar shugabancin Majalisar Dattawan, wanda kuma masu lura da al’amuran siyasa ke ganin yanada goyon bayan ‘yan Majalisar masu yawa a lokacin, to sai dai Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga cikin lamarin tareda samar da maslaha a tsakaninsu inda Sanata Barau ya amince da janyewa Sanata Godswill Akfabio.

Abin jira agani shine shin wannan shugabanci zai dore ko kuwa zai fuskanci bore, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories