Wednesday, August 26, 2026
HomeRa'ayiShin su wanene ke tsoron El Rufai a Gwamnatin Tinubu? ...

Shin su wanene ke tsoron El Rufai a Gwamnatin Tinubu? Kamaluddeen Shawai

Date:

SHIN SU WAYE KE TSORAN ELRUFAI A GWAMNATIN TINUBU NE?



31/8/2023

Ba sabon labari bane cewar irin yadda ake cigaba da kutsiri tsoma gami da cece- kuce da ‘yan Najeriya ke faman yi kan rashin tantacewar da Majalisar Dattijan Najeriya tayi wa wasu mutane uku ciki harda Malam Nasir El-Rufa’i da Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya aike musu don tabbatar dasu ministoci a cikin kunshin majalisar zartarwar Najeriya na cigaba da sànya àyar tambaya a zukatan al’umma.

A kwai dai tarin tamboyin da al’ummar Najeriya musamman a yakin arewacin kasar ke matikar muradin samun amsar su cikin hanzari, tambayoyin da kuma suke da daure kai da sarkakiya a tattare dasu.

Ta tabbata, cewar akwai makirce- makirce- a duk abubuwan da suka biyo bayan dakatar da tantance Malam Nasir El-Rufa’i a matsayin minista a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

A yayin da Malam Nasir El-Rufa’i, Wanda shine Gwamnan jihar Kaduna da ke Arewa maso yammacin Najeriya a baya -bayan nan da ya sauka, ya tsinci kansa a wani yanayi irin na yaudara da mafi yawan al’ummar Najeriya ke danganta irin kutungwilar da aka kitsa don yaudara da sunan rahoton tsaro da bangaren jami’an tsaron Najeriya.

Za a iya tabbatar da hakan ne kawai, idan aka yi waiwaye da masu iya magana kan ce a don tafiya duba da tarin gudunmawar da Malam ya bayar wajen tabbatar da nasar kafa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

Da farko dai, Malam Nasir El-Rufa’i shine mutumin daya shige gaba- gaba wajen hada kafatalin gwamnonin yanking arewa maso yammacin Najeriya su bakwai don marawa tafiyar Bola Ahmad Tinubu baya zama Shugaban kasa.

Shine mutum daya tilo daya dinga kai gwauro ya kai mari wajen ganin ya hada dukkanin yankunan Najeriya shidda don tabbatar da Asiwaju ya kai labari na zamantowa Shugaban Najeriya a shekara ta 2023.

Har wa yau, El-Rufa’i shine wanda yayi tsayin daka wajen ganin mulki ya koma kudancin Najeriya domin ganin an tabbatar da adalci da kawo daidaito a zamantakewar al’ummar Najeriya.

El-Rufa’i ya kuma cigaba da yin kiraye -kiraye wajen ganin hakan ta tabbata tare da nunawa al’ummar Najeriya musamman yakin Arewacin kasar nuna halayyar dattaku wajen baiwa yankin Kudu dama a wannan karon su jagoranci kasar.

Bayanai da suka tabbata sun yi nuni da cewar wasu daga cikin dattawan Arewa sun gayyaci Malam Nasir El-Rufa’i a gidan wani fitacce kuma mai fada aji a yankin Arewa, a’ inda aka bukace Nasiru daya siyo form na tsayawa takarar Shugabancin Najeriya don samun goyon baya, nan take El-Rufa’i ya ce an rufe siyan.

Dattawan sun tabbatar masa da cewar duk da hakan, zasu yi duk Mai yiwuwa wajen samo masa form din tsayawa takarar, abin da suke da bukata kawai ya amsa na cewa zai tsaya.

Malam Nasir El-Rufa’i ya tabbatarwa dattawan da ke a wancen zauran da suke tattaunawar cewar basi da bukata Kuma shi yana goyon bayan mulki ya koma kudancin Najeriya.

Ya Kuma Kara jaddada musu cewar shi ya na Kam bakansa na marawa Bola Ahmad Tinubu baya.

A nan ne aka tashi baram- baram, Kuma wannan ne ya haifar da Kalaman da ‘yan Najeriya suka fara ji daga bakin Malam Nasir El-Rufa’i na cewar babu dattawa domin an san dattijawa ne da tsayawa akan abinda ya ke shine daidai domin tun ba yanzu bane yankin ya amince da mika mulki zuwa kudancin Najeriya, a don haka lallai, akwai bukatar cika wancen alkawarin.

Malam Nasir El-Rufa’i bai tsaya nan ba, ya cigaba da tsayawa tsayin daka tare da himmatuwa wajen cika alkawarin da ya dauka tun bayan da Bola Ahmad Tinubu ya bukaci da yayi watsi da kudirin sa, na barin Najeriya bayan kammala zaben shekara ta 2023 zuwa kasashen waje don karo karatu.

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya kafe kai da fata sai El-Rufa’i ya yi aiki dashi don taimaka masa wajen dai-daita Najeriya da a yanzu take bukatar jajirtattu irin su Mal Nasir El-Rufa’i.

Tun kafin sannan, El-Rufa’i ya sanar da cewar shi Kam ba zai Kara rike wani matsayi ba, to amma daga bisani bayan matsin lamba a fili da boye daya fuskanta musamman daga bangaren Bola Ahmad Tinubu na lallai sai ya janye wancen Kalaman tare da yin alkawarin yin aiki dashi ya sanya El-Rufa’i yin zabi na E ko A’A.

Daga karshe Malam Nasir El-Rufa’i bayan matsi da kiraye-kiraye gami da rokon da Tinubu ya yi masa na ya hakura suyi aiki tare ya amince kuma yace muje zuwa.

Hakan ya sanya maganganu mara kai da gindi da aka dinga jifan Malam Nasir El-Rufa’i na yin amai ya lashe ba tare masu wadancen Kalaman sun bibiyi abunda ya faru ba a yayin da Bola Ahmad Tinubu ya bukaci Mal Nasir El-Rufa’i janye wadancen Kalaman na yin ritaya daga siyasa.

Bayan amincewar da Malam Nasir yayi ba tare da wani jinkiri ba, sai El-Rufa’i ya fara aikin tallata Bola Ahmad Tinubu gadan-gadan wajen yin tsaiwar daka don cika alkawarin da ya dauka na taimakawa tare da mara masa baya.

El-Rufa’i yayi fafutuka mai tarin yawa tare da Sanya kafar wando da duk wani ko wata kungiya da take kokarin kawo tasgaro ga nasarar Bola Ahmad Tinubu tare da tabbatar da ganin ya kawar da duk wani kulli da aka kulla wanda zai kai ga rasa kujerar Shugabancin Najeriya da Tinubu ya ke nema.

El-Rufa’i ya lallashi ‘yan uwansa da ke yankin Arewacin Najeriya na yin adabo da Shugabancin Najeriya a maimakon haka sai ya cigaba da tunatar dasu cewa a tuna alkawarin cen da aka dauka na mikawa kudancin Najeriya mulki.

Don haka, a kwarai bukatar marawa Tinubu da ke kudancin Najeriya baya.

Malam Nasir El-Rufa’i ya kuma futo na futo da tsarin nan na sabunta takardun kudade da Gwamnan babban bakin Najeriya a wancen lokacin ya bullo da shi a karkarshin jagorancin tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a’ inda ya har kotun koli ya tinkara don kalubalantar shirin, duk kuwa da dangantakar sa da tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Bugu da kari, Mal Nasir El-Rufa’i da sauran wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC a Najeriya na ganin wancen matakin da babban bakin ya dauka wata alama ce ta bita da kulli domin an kitsa hakan ne don kayar da Bola Ahmad Tinubu a zaben shekara ta 2023.

Ta Kuma Kara futowa fili karara cewar, Malam Nasir El-Rufa’i shine mutum daya tilo daya fito bainar jama’a yana mai cewar akwai wasu tsiraru a fadar tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da baso son nasarar Bola Ahmad Tinubu wajen kaiwa gaci a zaben shekara ta 2023 tare da zama Shugaban Najeriya.

Ko mahassadan Malam Nasir El-Rufa’i sun shaida tare da tabbatar da cewar, ya taka muhimmiyar rawar da ba Wanda ya taka irin ta wajen samun nasarar Shugaba Bola Ahmad Tinubu duk da kalamai na batanci da zage- zage da kage da habaici da sharrace- sharrace da amfani da addini da yarfe irin na siyasa duk dai domin a bata Malam Nasir El-Rufa’i yayin yakin neman zabe da bayan samun nasara musamman a daidai lokacin da ake kokarin tabbatar dashi minista.

Kuma wannan bai karya masa gwiwa ba, illa ma Hakan ya kara bashi kuzari da himma wajen cimma abinda ya Sanya agaba.

Ko shakka babu, Malam Nasir El-Rufa’i bashi da na biyu a kacokan cikin kunshin gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu kuma tarishi ba zai manta da irin tsaka mai wuya da ya shiga don ganin Bola Ahmad Tinubu ya dare Shugabancin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da sanya hannun wasu daga makusantan Shugaba Bola Ahmad Tinubu da kitsa kutungwilar jinkirta tantance Malam Nasir El-Rufa’i wajen kasancewa minista tare da yunkurin wulakantashi a bainar jama’a don cimma wasu muradan su na Kashin kansu.

Idan har wadannan jami’an gwamnatin wadanda suke makusan tan Asiwaju zasu Kai ga kitsa hakan ga Malam Nasir El-Rufa’i, abin tambaya nan shine Ko Shin ina Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ke yayin da ake kokarin muzanta El-Rufa’i?

Shin Bola Ahmad Tinubu ya ganin haka daidai ne a kyale a cigaba da yi wa Malam Nasir El-Rufa’i rikon sakainar Kashi?

Su waye ke tsoron shugowar El-Rufa’i cikin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu?

Shin hakan dai- dai ne a lokacin Mal Nasir ke matikar bukatar dauki da kariya da magauta Shugaba Tinubu ya yi biris ya kyale shi?

Shin mutumin daya bayar da irin wancen gagarumar gudunmawar yayin da mafi yawa ke gudu tare da ja da baya da nuna dardar ya kamata ayi watsi da shi?

Ko shin Bola Ahmad Tinubu ya na ganin soki burutsin da makusantan sa ke yi na danganta wasu kalamai ga Nasir El-Rufa’i Bolan ya gamsu dasu.

Kada fa zancen masu shagube ya zama gaskiya na cewar Shugaba Tinubu kayi amfani da Mal Nasir El-rufai ne domin samun nasara? Idan Kuma ba haka bane to kuwa lallai akwai bukatar Bola Ahmad Tinubu ya yi hanzari wajen kare kima da martabar Mal Nasir Elrufai.

Kuma babban abin tsoron ma a nan shine, ba Malam Nasir El-Rufa’i abin zai shafa ba, wannan halayyar wacce ke kama data yaudara musamman duba da yadda masu fashin bakin harkokin siyasa ke dangantawa da anci moriyar ganga ka iya kaiwa ga shafar mutunci da kima ta shi kansa Shugaban kasa Tinubu.

Domin kuwa al’ummar yankin Arewacin Najeriya zai yi wuya su sake amincewa tare da sakan- kancewa da duk wanda ya siffatu da irin wadancen halayen ko ya aikata irin yadda ta faru ga Mal Nasir El-Rufa’i wanda ya sadaukar da rayuwarsa da Jin dadin sa don cikawa don cikar burin Bola Ahmad Tinubu Amma daga baya ya tashi a tutar famfamfam.

Idan har Bola Ahmad Tinubu zai iya yin biris da abinda Mal Nasir Elrufai yayi masa, to shakka babu da sauran rina a kaba.

Me iya aka iya kaiwa ga tantamce Nyemsom Wike na jihar Rivers duk da cewar Dan jam’iyyar hamyya ne a PDP?

Mutumin daya futo karara ya bayyana cewar jihar sa ta mabiya addinin Krista ce Kuma Babu wani mahaluki da ya isa yasa ya janye Kalaman sa.

Me yasa Shugaban Majalisar Dattijan ya dare Shugaban Majalisar duk da zarge zargen handama da baba kere na sama da biliyan dari Amma Bola Ahmad Tinubu ya yarda dashi a kujerar.

Idan har za iya dauko Wike Mai zai hana a dauko Kwankwaso?

Alummar yankin Arewacin Najeriya dai sun zuba idanu za Kuma su cigaba da bibiyar irin yadda salo da kamun ludayin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ke cigaba da zakudawa.

Kazalika, masana na cigaba da yin sharshi kan nagarta da cancata na wasu daga cikin ministocin da aka nada a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu a inda musamman a yakin Arewacin Najeriya ake ganin tamkar wani makirci ne aka shiryawa yankin na kin zakulo fitattu,kwararru, jajirtattu,masu kishi wadanda alummar yankin ne a zukatan su kasancewa ministoci.

A yayin da kukkanin wadancen al’amuran ke cigaba da wakana, kamata yayi Shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi duba irin na tsanaki ya nutsu yayi waiwaye sosai tare da yin duk mai yiwuwa don kare kima da martabar Mal Nasir El-rufai daga abokan gaba ‘yan siyasa da magabta daga kowanne bangare.

Domin ko shakka babu, Malam Nasir El-Rufa’i ba shine yayi asara ba, al’ummar Najeriya ce tayi asarar namijin duniya, gwani kuma gwarzo hazikin mutum, jajirtacce mai aiki tukuru.

Kamar yadda masharhanta ke nuni da cewar sauran kiris a tafka babban kuskure da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu tayi ko take shirin yi na cigaba da rikon sakainar Kashi ga batun Malam Nasir El-Rufa’i, duba da duk irin gudanarwar daya bayar wajen tabbatar da nasarar gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

Shin ya kyauta Bola Ahmad Tinubu ya bari ayi wa Mal Nasir El-rufai haka komai me yayi masa a baya?

Daidaikun mutane da kungiyoyi sun ta kawo suka na zarge zargen karya da kalaman batanci wandanda dukkanin su basu da tushe ballantana makama. Babu kuma kanshin gaskiya ciki sai hassada da sharri.

An kitsa sune domin bata suna da hassada ga Mal Nasir El-rufai a idanun al’umma, adai-dai lokacin da a hannu daya kuma tauraruwar sa ke cigaba da haskaka wa a Kudu da Yamma da Gabas da Arewa.

Ko mai dai za ace , makiyansa da mahassadan sa sun sani sarai cewar, Mal Nasir El-Rufa’i ba matsoraci bane,ba malalaci bane,kwararru ne,jarumi ne kuma duk abinda aka abashi yayi zai yi shi fiye da tunanin wanda ya bashi aikin.

Malam Nasir El-Rufa’i ba ya shakkar badin gaskiya komai dacin ta kuma baya tsoron me zai je yazo indai na batun gaskiya ne.

Mal Nasir El-Rufa’i shine maganin mutanen munfukai da ‘yan ta-da zaune tsaye musamman masu san kansu da rura wutar kabilanci da addini.

Idan kana da ja , za iya bibiyar irin tarishin daya kafa lokacin da yake hukumar cefanar da kaddarorin gwamnatin tarayya wato BFE da Kuma lokacin da ya zama ministan babban birin tarayya Abuja dama lokacin da yake Gwamnan jihar Kaduna.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories