Wednesday, August 26, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu yayi alkawarin kawo karshen hauhawar farashin kayyaki

Shugaba Tinubu yayi alkawarin kawo karshen hauhawar farashin kayyaki

Date:

Shugaba Tinubu yayi alkawarin kawo karshen hauhawar farashin kayyaki

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yace gwamnatinsa zatayi duk mai yiwuwa wajen karshen hauhawar farashin kayan masarufi tareda bunkasa tattalin arzikin ‘yan kasa cikin shekara mai kamawa.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin dayake gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 gaban tagwayen majalisun Dattawa data Wakilai a yammacin larabar nan.

Shugaban ya gabatar da kasafin Naira Tiriliyan 27 da digo 5 bisa hasashen za’a saida man fetur akan dala 77.96 daga ganga miliyan 1.78 a duk rana, inda ake saran farashin dala zai kasance akan Naira 750.

Kasafin wanda ake saran zaifi maida hankali bangaren tsaro, an ware Naira tiriliyan 9.92 abangaren ayyukan yau da kullum, sai kuma bangaren manyan ayyuka da aka ware masa Naira tiriliyan 8.7.

Acikin kunshin kasafin, an ware Naira tiriliyan 8.25 wajen biyan basussukan da ake bin Najeriya.

Shugaba Tinubu yace zasu sassauta hauhawar farashi da kaso 21.4 cikin dari.

Kasafin kudin dai yazo a lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin halin kuncin rayuwa sakamakon tsadar rayuwa da rashin tabbas abangaren tsaro.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories