Wannan hukunci bazai kashe mana gwiwa wajen cigaba da yiwa al’umma aiki ba…
Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa hukuncin da kotun sauraron korafin zaben Gwamna tayi bazai kashe musu gwiwar cigaba da gudanar da ayyukan raya kasa ga al’ummar Kano ba.
Gwamnan yayi wannan jawabi ne lokacin wani taron Manema labarai daya kira a fadar Gwamnatin Kano.
Gwamna Yusuf yace, kasancewar Alkalan Mutanene zasu iyayin kuskure, yasanya bayan nazari da sukayi suka gano kura kurai a hukuncin, a don haka zasu daukaka Kara.
Gwamnan yakara da cewa “Mun umarci lauyoyinmu dasu gaggauta daukaka Kara domin dawo da hakkin al’umma”.
Gwamnan yace, abune dayake afili ya lashe zaben da akayi a watan Maris da kuri’u mafiya yawa, inda yasamu sama da kuri’a miliyan daya, amma bangaren hamayya suka garzaya gaban kotu inda suka kalubalanci wannan nasara ta al’ummar Kano, acewar Gwamnan.
A ranar laraba ne kotun sauraron korafin zaben Gwamna ta ayyana Dr Nasiru Yusuf Gawuna amatsayin wanda ya lashe zaben 9 ga watan Maris bayan da tace anyi aringizon kuri’u fiyeda dubu 165.