Kungiyar ‘Yan Jaridar Harkokin Ruwa ta Najeriya (NMJ), wadda ta ƙunshi mambobi daga ƙungiyoyin kafofin watsa labarai na ruwa daban-daban, za ta baiwa Babban Kwamturola-Janar na Hukumar Kwastam na Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi, lambar girmamawa ta “Gwarzon Shekara a Harkokin Ruwa na 2024” a birnin Legas.
A cewar wata sanarwa da Sakataren Kwamitin shirye-shiryen bayar da kyautar, Innocent Orok, ya sanya wa hannu, ya ce an cimma wannan matsaya ne daga dukkan ‘yan jaridar da ke daukar rahotanni a bangaren harkokin ruwa, bayan da suka amince da jagoranci mai ban sha’awa da nasarorin CGC Adeniyi, tun bayan da ya hau kujerar shugabanci.
“Ba bu shakka ka gyara kuma ka sake farfado da Hukumar Kwastam a dukkan bangarori. Kokarinka da ke da ban mamaki ya jawo maka kyaututtuka na ƙasa da na ƙasashen duniya, hakan kuma ya kawo wa Hukumar da Nijeriya daukaka.” Yace.
“Mu ‘yan jaridar harkokin ruwa, wadanda suka haɗa da jaridun bugawa, na lantarki, da kuma na yanar gizo, muna farin cikin kasancewa cikin wannan tarihin tare da kai a matsayin abokan ci gaba,” in ji Innocent Orok.
Haka zalika, shugaban kwamitin shirye-shiryen bayar da kyautar, Dele Aderibigbe, ya bayyana cewa wannan karramawar tana da matuƙar muhimmanci, ya kara da cewa “wannan shi ne karo na farko a cikin bangaren harkokin ruwa da dukkan ‘yan jarida da ke rufe wannan fanni suka haɗu don karrama wani shugaba da ya cancanta sosai, wanda ya daukaka hukumar Kwastam da kuma Najeriya baki ɗaya ta hanyar jagoranci mai ma’ana, kwarewa, da kishin ƙasa.”
Ya jaddada cewa wannan kyauta na da nufin kafa tubalin daidaito ga sauran hukumomin gwamnati, domin nuna cewa ‘yan jaridar harkokin ruwa suna bibiyar ayyukan su.
Za a gudanar da bikin bayar da kyautar a ranar Alhamis, 16 ga Janairu, 2025, a dakin taro na Apapa Port Command.