Thursday, April 30, 2026
HomeKasuwanci'yan kasuwa dake kasuwanci a filin Idi sun gudanar da Sallar Alqunut

‘yan kasuwa dake kasuwanci a filin Idi sun gudanar da Sallar Alqunut

Date:

‘yan kasuwa dake kasuwanci a filin Idi sun gudanar da Sallar Alqunut


‘yan kasuwa da rusau tashafa a filin Idi sun gudanar da Sallar Alqunut domin neman taimakon Allah akan masifar data samesu na rushe musu gurin kasuwanci da gwamnatin Jihar Kano tayi.

Dayake jawabi ga ‘yan jarida Jim kadan bayan kammala Sallar, daya daga cikin jagororin ‘yan kasuwar ta filin Idi Muhammad Sadiq Abdullah yace, duk wanda yamallaki shago a filin na Idi yacika duk wata ka’ida da Masarautar Kano ta shimfida kasancewar filin na Masarautar Kano ne.

Yace ” yakamata gwamnatin Kano ta sake duba lamarin la’akari da irin dukiya ta biliyoyin Naira da muka narka, kuma munyi shine a bisa ka’ida da gwamnati ta shimfida kuma fili na masarauta ne” inji Muhammad Sadiq.

Yacigaba da cewa, rushe wannan guri da suke neman abinci ya jefa al’umma da dama cikin masifa.

A makwanni biyu da suka gabatane dai gwamnatin Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf ta rushe shagunan dake masallacin na Idi da hujjar an ginasu ba bisa ka’ida ba.

Sai dai bayanai sun nuna cewa tun lokacin tsohon Sarkin Kano Muhd Sunusi na biyu Masarautar Kano ta bukaci gwamnatin Kano data bata dama domin baiwa ‘yan kasuwa damar gina shaguna a kewayen masallacin na Idi domin kawo karshen ayyukan bata gari da miyagun mutane dake amfani da filin wajen aikata miyagun laifuka.

Abin jira agani shine, gwamnatin zata saurari koken ‘yan kasuwar tareda zama dasu, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories