Sunday, August 30, 2026
HomeDa Ɗumi-ƊumiYanzu Yanzu: Kotu ta Kori karar Kabiru Gaya

Yanzu Yanzu: Kotu ta Kori karar Kabiru Gaya

Date:

Kotun sauraron korafin zaben ‘Yanmajalisa r dattawa ta kori karar da Sanata Kabiru Gaya yashigar gabanta yana kalubalantar nasarar da Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila yasamu amatsayin Sanatan Kano ta Kudu a zaben shekarar 2023.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Justice RO Odogu tace, Sanata Kabiru Gaya yagaza bada hujjoji gamsassu da zasu sanya kotun canja wancen sakamako daya ayyana Sanata Kawu Sumaila amatsayin wanda ya lashe zaben Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu.

Kotun ta Kuma cishi tarar N200,000, Wanda zai baiwa kowanne daga cikin wadanda yashigar Kara sakamakon bata musu lokaci da yayi.

Tsohon Sanatan dai zai biya tarar ne ga Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, da Jam’iyyar NNPP da kuma Sanata Kawu Sumaila.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories