Saturday, June 27, 2026
HomeSiyasaYanzu Yanzu: Kotun sauraron korafin zabe ta baiwa Hafiz Kawu nasara

Yanzu Yanzu: Kotun sauraron korafin zabe ta baiwa Hafiz Kawu nasara

Date:

Yanzu yanzu

Kotun sauraron korafin zabe ta soke zaben da akayiwa Hon Mukhtar Yarima amatsayin Danmajalisar tarayya mai wakiltar Tarauni.

Kotun mai alkalai uku, ta tabbatar da Hon Hafiz Ibrahim Kawu na Jam’iyyar APC amatsayin wanda ta mikawa kujerar bisa dogaro da hujjar gabatar da sakamakon bogi na Firamare da Danmajalisar Yarima yayi.

Yarima dai ya tsaya ne karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP a zaben da akayi a watan Fabarerun daya gabata.

Jim kadan bayan fitowa daga kotun, lauyan Mukhtar Yarima Barista Rabiu Sadiq yace sun karbi wannan hukunci kuma zasu daukaka kara.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories