Sunday, August 30, 2026
HomeDa Ɗumi-ƊumiYanzu Yanzu: Kotun sauraron korafin zaben 'Yanmajalisa ta tabbatarwa Iliyasu Kwankwaso nasara

Yanzu Yanzu: Kotun sauraron korafin zaben ‘Yanmajalisa ta tabbatarwa Iliyasu Kwankwaso nasara

Date:

Yanzu Yanzu: Kotun sauraron korafin zaben ‘Yanmajalisa ta tabbatarwa Musa Iliyasu Kwankwaso nasara

Kotun sauraron korafin zaben ‘Yanmajalisa ta Kwace Kujerar Danmajalisar tarayya mai wakiltar Kura Madobi Garun Malam daga hannun Hon Yusuf Umar Datti na Jam’iyyar NNPP inda tabaiwa Hon Musa Iliyasu Kwankwaso na Jam’iyyar APC, bisa hujjar cewa bai ajiye aikin sa ba.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Justice Ngozi Flora Azinge, ta kuma ce shiga zaben fitar da gwani da Yusuf Datti yayi ya Saba doka.

Kotun ta umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC data baiwa Musa Iliyasu Kwankwaso shaidar lashe zabe kasancewar shine yazo na biyu a kuri’u mafiya yawa.

A ranar 25 ga watan Fabarerun daya gabata ne hukumar zabe ta INEC ta ayyana Hon Dr Yusuf Datti amatsayin wanda yalashe zaben Danmajalisar tarayya mai wakiltar Kura, Madobi, Garun Malam, lamarin daya sanya Musa Kwankwaso tafiya kotu domin kalubalantar matakin.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories