Sunday, August 30, 2026
HomeDa Ɗumi-ƊumiYanzu Yanzu:Kotun sauraron korafin zaben 'Yanmajalisa ta kori karar Sunusi Kiru yashigar

Yanzu Yanzu:Kotun sauraron korafin zaben ‘Yanmajalisa ta kori karar Sunusi Kiru yashigar

Date:

Kotun sauraron korafin zaben ‘Yanmajalisa dake zamanta a Kano ta tabbatarwa Hon Abdulmuminu Jibril Kofa nasarar daya samu a zaben da akayi a watan Fabarerun daya gabata.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Justice Ngozi Flora, tace mai kara (Muhammadu Sunusi Kiru) da Jam’iyyar sa ta APC sun gaza gamsar da kotun zargin da sukeyi na rashin ajiye aikin wanda suke kalubalanta da kuma aringizon kuri’a, abinda kotun tace irin wannan batu yana bukatar kwararan hujjoji da zasu gamsar da kotun.

Da wannan hukunci dai, kotun ta kori karar da Hon Sunusi Kiru da Jam’iyyar APC suka shigar, inda ta bukaci yabiya tarar Naira dubu 100 ga Hon Kofa da Jam’iyyar sa ta NNPP da kuma hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC bisa bata musu lokaci da yayi.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories