Tuesday, August 25, 2026
HomeSiyasaZaman Lafiyar Jihar Kano Shine Burinmu~ Rarara

Zaman Lafiyar Jihar Kano Shine Burinmu~ Rarara

Date:

Zaman Lafiyar Jihar Kano Shine Burinmu

Mashahurin mawakin siyasarnan Dauda Adamu Abdullahi da akafi sanida (Rarara) yace basuda burin daya wuce dorewar zaman lafiya da karuwar arzikin jihar Kano.
Rarara ya bayyana hakan ne lokacin wani taron manema labarai da masu ruwa da tsaki a masana’antar shirya fina finai ta kannywood suka kira a yammacin litinin.
Rarara yace” lokacin da kotun sauraron korafin zaben Gwamna tabamu nasara bamuyi wani abu na tada hankali ba da sunan murna, hasalima lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tace bamune mukayi nasara ba hakura mukayi tareda tafiya kotu domin neman hakki”.
Rarara ya kumayi kira ga magoya bayan Jam’iyyar APC a Kano dasu kasance masu da’a da bin doka da oda kafin da lokacin da kuma bayan hukuncin kotun Koli.
Dayake jawabi tunda fari, tsohon babban daraktan hukumar tace fina finai da dab’i ta jihar Kano Ismail Na’Abba Afakallah, ya yabawa hukumomin tsaro musamman ‘Yansanda da DSS akan yadda suke gudanar da ayyukansu na tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma, inda ya bukaci dasu kara kaimi gurin tsaurara tsaro musamman ma ganin ana dakon hukuncin kotun Koli kan zaben Gwamnan Kano.
Taron manema labaran ya samu halartar masu bada umarni da taurari da mawaka da sauran ‘yan masana’antar ta Kannywood.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories